Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar Juma’a, 22 ga watan Yuli, ta kama wata matar aure ‘yar shekara 20, bisa laifin kashe mijinta mai shekaru 38 da haihuwa. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.
A cewar DSP Suleiman Nguroje, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, wacce ake zargin mai suna Caroline Barka, ‘yar unguwar Angwan Tamiya, a karamar hukumar Madagali, ta yi artabu da mijinta mai suna Barka Dauda, bayan wata takaddama da ta barke a tsakaninsu. Marigayin ya dawo gida a cikin buguwa na barasa, ya fada kan Jaririnsu ‘yar shekara daya da ke kwance.
'Nan take mayar ta fusata wadda tun farko take cike da fushinsa na rashin wadatar da ita da abinci da kayan masarufi a matsayinsa Miji, wanda ake zargi sun yi artabu da juna wanda ya yi sanadin ta daba wa Mijin wuka. Sakamakon haka ya fadi a sume kuma daga baya aka garzaya da shi Asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Nguroje ya kara da cewa ‘yan sanda sun cafke wanda ake zargin ne a karamar hukumar Madagali sakamakon rahoton da aka samu daga wani dan uwan mamacin.
Ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP SK Akande, ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (bincike) da ya dauki nauyin lamarin tare da tabbatar da gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya.