Yan bindiga sun sace jami'an Yan sanda 10 da ke hanyar dawowa daga zaben jihar Osun


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa guda 10 da ke kan hanyarsu ta dawowa daga aikin zabe a jihar Osun. Shafin isyaku.com ya samo.

Wata majiya ta shaida wa jaridar The Guardian cewa an yi garkuwa da jami’an ne a Obajana, cikin Kogi, a ranar Lahadi, 17 ga Yuli, 2022.

Majiyar ta ce; 

“A ranar 17 ga Yuli, 2022, da misalin karfe 11:05 na safe, an samu bayani daga jami’in ‘yan sanda (DPO) na Obajana cewa an ji karar harbe-harbe a kan hanyar New By-Pass, kusa da Trailer Park, PTI Obajana. Nan take DPO ya tattaro ’yan sintiri zuwa wurin, inda suka hadu da wata farar bas mai dauke da mutane 18 mai lamba GWA 295 YR, wani Usman Abdullah ne ya tuka shi da mutane shida.

“Mutane bakwai sun bayyana kansu a matsayin jami’an ‘yan sandan jihar Nasarawa da suka dawo daga zaben gwamnan jihar Osun. Sun bayyana cewa motar tasu ta samu matsala, kuma yayin da suke kokarin gyara motar, wasu dauke da makamai sun fito daga cikin daji suka yi awon gaba da jami’ai 10.”

Rahotanni sun ce an baza jami’an da ke yaki da masu garkuwa da mutane yankin domin bin diddigin masu laifin. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN