Dalilin da yasa muka fadi zaben Gwamnan Jihar Osun, daga karshe Shugaban Jam'iyyar APC Adamu ya bude zancen, ya yi hasashen abinda zai faru


Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana dalilan da suka sa jam’iyyar ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Osun a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli. 

Adamu ya ce rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar APC ne ya jawo asara, ba wai jam’iyyar ba za ta iya yin nasara ba a zaben.

Shugaban na APC ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Ademola Adeleke ne ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 403,371 inda ya doke dan takarar jam’iyyar APC, Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC da ya samu kuri’u 375,027.

Da yake magana kan dalilin da ya sa Oyetola ya yi rashin nasara, Adamu ya ce:

“Mun rasa tseren ne ba don ba mu iya ba amma saboda rikicin da ke ciki. Mun samu gagarumin taron magoya baya kwanaki kadan kafin zaben a Osogbo. Babu wanda zai taba tunanin cewa za mu fadi zabe.

Ya lura cewa al’ada ce ta rayuwa mutum ya rasa wani abu da yake bukata da gaske, inda ya ce jam’iyyar ta amince da shan kaye da gaskiya kuma ta koyi darasi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN