Yadda wata mata ta damke al'aurar dan takarar shugaban kasa a wajen kampen (Bidiyo)


Bidiyon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Roots, Farfesa George Wajackoyah, ya nuna yadda wata mata ta sharbo al'aurarsa lokacin da yake yakin neman zabe ya bazu bayan an yada shi ta yanar gizo. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa hakan ya faru ne a yayin da jama'a suka yi wa dan takarar shugaban kasar Kenya dafifi a lokacin da yake yakin neman zabe a bayan wata babbar mota.

Dan takarar shugaban kasa mai cike da cece-kuce yana sayar da ajandarsa kafin wata mata a cikin jama'a ta damke al'aurarsa da karfi ta tilasta masa ya mayar da martani.

Mai rike da tutar jam’iyyar Roots ya ja da baya, yayin da jami’an tsaronsa su ma suka fara aiki, lamarin da ya tilasta wa matar ta janye hannunta da sauri. 

"Usinishike hivyo (Kada ki ta…ďa ni haka)," Wajackoyah ya nuna rashin gamsuwa sosai bayan da matar ta kama al'aurarsa.

"Sasa huyu ananishika sehemu yangu ya nyeti (Yanzu wannan tana kama al'aurana)," Wajackoyah ya gaya wa taron cikin dariya.

Kalli bidiyon a kasa....

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN