Tikitin Musulmi da Musulmi: Shugabannin Kiristocin jam'iyar APC na Arewa za su nemi wani dandali


Shugabannin kiristocin Arewa a jam’iyyar APC sun cimma matsaya kan cewa tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi na da raba kan jama’a, don haka suna neman hanyar da za su bi don samun mafita. Shafin isyaku.com ya samo.

Legit.ng ta ruwaito cewa ‘Yan siyasar Kiristocin Arewa sun yi wannan tsokaci ne a yayin wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a 29 ga watan Yuli, wanda ya samu halartar Babachir Lawal, Yakubu Dogara, da Elisha Abbo da dai sauransu.

‘Yan jam’iyyar APC a taron sun yi nuni da cewa shirin Tinubu-Shettima na 2023 rashin adalci ne.

‘Yan siyasar sun kuduri aniyar cewa za su fito da wani tsari na kasa baki daya a Najeriya wanda zai dauki nauyin kiristoci da Musulmi, wanda zai kai ga cimma burin dunkulewar kasa baki daya.

Sun ce yayin wani taron koli tsakanin addinai, za a sanar da ‘yan Najeriya shawarar da suka yanke kan wannan dandali.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN