Wata kotun Majistare da ke Iyaganku da ke zamanta a Ibadan a ranar Juma’a ta bayar da belin wasu mutane uku a kan kudi Naira miliyan 5 kowannensu bisa zargin satar buhunan shinkafa 600 na Naira miliyan 17. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
NAN ta ruwaito cewa ‘Yan sandan sun gurfanar da Afeez Bello, mai shekaru 40; Obitayo Makinde mai shekaru 56 da kuma Isiaka Ibraheem mai shekaru 34 da hada baki da kuma sata.
Wadanda ake tuhumar dai sun musanta aikata laifin.
Alkalin kotun, SH Adebisi, ya kuma umurci wadanda ake kara da su gabatar da wadanda za su tsaya masu guda biyu ko wannensu a daidai adadin.
Adebisi ya ce dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya zama ma’aikacin gwamnati a kan GL10 yayin da na biyun ya kasance mai mallakar kadarori a karkashin ikon kotun.
Ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Satumba domin sauraren karar.
Tun da farko, Dan sanda mai shigar da kara, Insp Opeyemi Olagunju, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne suka sace shinkafar a lokacin da ake jigilar kayan daga Yola a Adamawa zuwa Ibadan.
Olagunju ya ce Bello, Makinde da Ibraheem a ranar 13 ga Afrilu sun sace buhunan shinkafa 600 na Funso Adebowale na Naira miliyan 17.
Ya ce laifin ya sabawa sashe na 383 kuma hukuncinsa a karkashin sashe na 390 (9) da 516 na dokokin jihar Oyo na shekarar 2000.