Yanzu yanzu: Kotu ta tsare matar aure bisa zargin yiwa matar makwabcinta cin mutuncin raini


A ranar Juma’a ne aka gurfanar da wata matar aure mai suna Aisha Abubakar ‘yar shekara 35 a gaban wata kotun shari’ar Musulunci a Kano bisa zarginta da laifin cin zarafin matar makwabcinta. Shafin isyaku.com ya samo.

Rundunar ‘yan sandan ta tuhumi Aisha da ke zaune a unguwar Rimin Auzinawa Quarters Kano da laifin cin zarafi da hargitsa jama’a.

Alkalin kotun, Isma’il Muhammed-Ahmed wanda ya bayar da umarnin, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Agusta domin ambatonsa.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insp Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa Khalid Sale ya kai kara a ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki a ranar 11 ga watan Yuli.

Mai gabatar da kara ya ce wanda ya shigar da karar ya yi zargin cewa da misalin karfe 6 na yamma da ya dawo daga aiki ya hadu da wanda ake kara a kofar gidansa tana zagi da cin mutuncin matarsa ​​ba tare da wani dalili ba.

Mai gabatar da kara ya ce laifin ya saba wa tanadin sashe na 165 na kundin laifuffuka.

Sai dai wanda ake tuhumar ta musanta aikata laifin

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN