Yadda wasu mutum 2 suka taushe mata mai ciki wata 7 suka yi mata fyade a jihar Arewa



An kama wasu mutane uku da ake zargi da yi wa wata mata mai ciki wata bakwai fyade a kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara. Shafin isyaku.com ya samo.

Wadanda ake zargin jami’an tsaron farin kaya na Najeriya sun kama Lawal Ibrahim mai shekaru 25; Mohammed Issa, 19; da Ibrahim Ahmed mai shekaru 20. 

An kuma bayyana cewa sun kuma yi wa wasu ma’aurata fashi tare da kwashe kayansu a ranar Talata, 5 ga Yuli, 2022 a Kauyen Woro.

Jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, Ayeni Olasunkanmi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an kama daya daga cikin mutane ukun mai suna Lawal a lokacin da yake kokarin sayar da wasu kayayyaki da aka sace a gidan ma’auratan.

Olasunkanmi ya ce; 

“An samu labarin fyade da fashi a ranar 5 ga watan Yuli a ofishin NSCDC Woro. An rahoto cewa laifin ya faru ne a kauyen Woro dake karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara da misalin karfe 2:00 na dare.

“Wadanda abin ya shafa; Wata mata mai ciki wata bakwai da mijinta an yi zargin cewa wadanda ake zargin sun kai wa gidan su da ke Woro hari. Matar mai ciki mai watanni 7 an yi zargin màharan sun yi mata fyade daga bisani suka sace wasu kayayyaki. 

“Bayan samun rahoton, mukaddashin kwamandan jihar, DCC Jonah Gabriel, ya bayar da umarnin a kamo wadanda suka aikata laifin.

“Duk da haka, radhin sa’a ya ci karo da wadanda ake zargin, yayin da daya daga cikinsu mai suna Lawal Ibrahim, jami’an mu ne suka kama shi a lokacin da yake kokarin sayar da kayayyakin da suka sace.

Da aka kama Lawal ya yi wasu kalamai na ikirari wanda a karshe ya kai ga cafke sauran mutanen biyun.

Tuni dai aka gurfanar da wadanda ake zargin a gaban wata kotun Area da ke Kaiama. Mai shari’a Usman Lukman ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali na tarayya da ke New Bussa har zuwa ranar 27 ga watan Yulin 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN