Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2023 ya kare zabinsa na Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takara.
Kafin bayyana Shettima a matsayin mataimaki, siyasar kasar ta dauki zafi kan batun zaben yan takara masu addini iri daya.
Yayin da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta yi gargadin hakan, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya su mayar da hankali kan cancanta fiye da addini ko kabila.
Dalilin zaben Shettima
Da ya ke magana kan dalilin zaben Shettima a matsayin abokin takararsa, Tinubu ya ce a duk rayuwarsa, cancanta, basira, tausayi, gaskiya, adalci da kwarewa ne ya ke amfani da su wurin zaben tawagarsa da masu taimaka masa.
Ya ce ya tuntubi mutane da dama game da batun mataimakin kuma ya godewa manyan mambobin jam'iyyar da abokansa na siyasa da manyan kasa "wadanda ke yi wa Najeriya kallo irin nasa."
Tinubu ya fayyace cewa bawa cancanta fifiko wurin shugabanci, da iya aiki tare da mutane shine babban abin da yasa ya zabi abokin takarar nasa.
"Ina sane ta tattaunawa da ake yi game da addinin abokin takara ta. Mutanen kirki sun mana magana kan hakan. Wasu sun shawarci in dauki kirista saboda kiristoci, wasu sun ce in zabi musulmi saboda al'ummar musulmi. Tabbas ba zai yiwu in yi duka biyun ba."
"Bangarorin biyu suna da dalilansu. Dukkkansu suna da gaskiya a ra'ayinsu. Amma dukkansu ba abin da Najeriya ke bukata ba kenan a yanzu. A matsayin shugaban kasa, ina fatan mulkan Najeriya don samun cigaba. Hakan na bukatar sabbin dabaru. Hakan zai bukaci abin da ba a yi ba a baya. Zai bukaci matakan siyasa masu wuyan zartarwa da ba a saba gani ba.
"Idan zan zama irin wannan shugaban kasar, dole in fara da zabin mataimaki na. Bari in dauki mataki ba don siyasa ba amma don bunkasa kasa da jam'iyyar mu don cigaba.
"A nan siyasa ta zo karshe, kuma ainihin jagorancin ya fara. Yau, na sanar da mataimaki na kuma ba don addini na zabe shi ba ko dan faranta wa wani bangare rai. Na zabe shi ne don na yi imanin zai taimaka min wurin gudanar da ingantaccen mulki, ba tare da la'akari da addini, kabila ko yanki ba."
Ga wanda ba su ji dadin zabin Tinubu ba, ya ce ba wai baya sauraren kokensu bane yana sane da su domin hakan na cikin mulki na gari amma ba kowanne lokaci bane addini da kabilanci zai rika jagorancin abin da za mu yi.
Domin cigaba dole mu yi watsi da wasu abubuwan baya mu daidaita siyasarmu kan turban cancanta da adalci ba wai yanki ba.