2023: Yanayin lafiyar jikin Tinubu, Kwankwaso ya aike muhimmin sako, ya ce..


Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, ya shawarci Bola Tinubu, mai rike da tutar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ya kula da lafiyarsa.

Da yake magana a yayin wata hira da Reuben Abati na AriseTV a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, shugaban NNPP ya ce yakin neman zabe yana da matukar kalubale kuma Tinubu yana bukatar daukar abubuwa cikin sauki domin lafiyarsa.

Ya ce:

"Idan ka ga abokina, Bola, ka gaya masa ya sauƙaƙa, kula da lafiyarsa sosai kuma ka tabbatar da cewa ... saboda ina son shi sosai, abokina ne," in ji shi.

Wannan yakin yana da matukar tsauri, yana bukatar kokari sosai da dai sauransu. Ina fatan zai Sami sauki domin mu ci gaba da fafutukar tabbatar da kasa daya mai karfi da wadata a Najeriya.”

Akwai damuwa game da lafiyar Tinubu tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban Najeriya na gaba.

A watan Agusta 2021, an yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC na cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya. Daga baya gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya musanta hakan inda ya ce Tinubu na da lafiya kuma yana da karfi.

Damuwar da aka samu game da lafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, bai hana shi zagayawa a fadin kasar nan domin tuntubar shugabanni a matakai daban-daban kan takararsa ta shugaban kasa ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN