Yadda kanin matar tsohon shugaban kasa dan shekara 30 ya auri matar wani tsohon Gwamnan Arewa mai shekara 50


Hajiya Hauwa, matar tsohon Gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai kenan a wadannan hotunan tare da karamin mijinta, Haliru Saad Malami. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

Nexus Photographer ne ya sanya hotunan a ranar Talata, 12 ga Yuli. 

Hauwa ta auri Malami, wanda shine Chief Executive Officer, ITBAN Global Resources LTd, a shekarar 2019, shekaru biyu bayan rasuwar Suntai.

Hauwa tana da shekaru 50 a Duniya yayin da Malami, wanda ke da shekaru 30 a Duniya, an ce kani ne ga Turai 'Yar'aduwa, matar marigayi Shugaban Najeriya, Umaru 'Yar'aduwa.


Idan dai za a iya tunawa, Suntai ya yi hatsarin jirgin sama a Yola a shekarar 2012 kuma an tafi da shi kasar waje don yi masa magani.

Ya rasu ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2017, a birnin Houston na jihar Texas ta kasar Amurka, bayan ya yi fama da raunukan hadarin jirgin da ya sa ya kasa yin wani aiki.



Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN