Ko da gaske ne Osinbajo ya nemi izinin Buhari don ya fice daga APC? Mataimakin Shugaban Kasa ya bude zancen karara


Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata wata takarda da ke nuni da cewa ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi izinin ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, inji rahoton jaridar The Nation.

Kamar yadda labarin ya samo asali ne daga wata takarda da aka bankado mai kwanan watan Yuni 24, 2022 mai lamba SH/VP/605/2./0, da ake zargin Osinbajo ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar neman izinin ficewa daga jam’iyyar APC.

Mataimakin Osinbajo na musamman ya mayar da martani

Da yake mayar da martani ga takardar, babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mista Laolu Akande, ya bayyana cewa takardar da abin da ke cikin ta na bogi ne.

Ya ce rubutaccen bayanin ba wai daga Osinbajo ​​ne ya fito ba.

Laolu ya ce:

“A ina ku ma kuke samun waÉ—annan abubuwan? Wa ya baka? Ko ta yaya, don guje wa shakku, memo É—in karya ne. VP bai rubuta irin wannan abu ba. "

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN