Da dumi-dumi: Kwankwaso ya zabi fasto matsayin mataimaki a zaben 2023 mai zuwa


Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa dan takararta na shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya zabi Bishop Isaac Idahosa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Alhamis inda ta rubuta cewa:

“Mataimakin shugaban kasanmu Fasto Bishop Isaac Idahosa daga jihar Edo.”

Tribune Online ta ce ta ruwaito cewa, Bishop Isaac Idahosa daga jihar Edo babban Fasto ne a cocin God First Ministry, wanda aka fi sani da Illumination Assembly da ke da hedikwatara Lekki LLC, Ajah, Legas.

Zabo faston dai na zuwa ne bayan rade-radin da ke yawo na cewa Kwankwaso na neman zabo tsohon gwamnan Anambra Peter Obi a matsayin abokin takara.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN