Type Here to Get Search Results !

Yadda Ɗan Acaɓa ya yi sanadin ceton ɗan shekara uku daga hannun masu garkuwa


Wata budurwa mai satar mutane yar shekara 23, Aanu Afolabi, ta shiga hannun dakarun yan sanda bisa zargin yunkurin garkuwa da wani jariri ɗan shekara Uku a yankin lkare Akoko, jihar Ondo.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa mahaifiyar jaririn, Misis Bamitale, ta barshi a shago domin zuwa ɗakko wasu kayayyakin amfani na gida a wani shago da ke layi na gaba.

Bayanai sun nuna cewa kafin ta dawo, wacce ake zargin ta shiga shagon ta ɗauki jaririn ta goya shi cikin sauri-sauri ta kama hanyar tsere wa.

Wane kokari ɗan Acaɓa ya yi?

Sai dai wani ɗan Acaɓa ya yi kuskuren kaɗe ta da Mashin ɗinsa yayin da take saurin tsallaka titi da jaririn da ta sato

Wata majiya da abun ya faru a gabanta, ta ce:

"Lokacin da Ɗan Acaɓa da wasu mutane da ke kusa suka yi sauri don taimaka mata da yaron da take goye da shi, nan ne fa ɗaya daga cikin mutanen da suka kawo ɗauki ta gane jaririn, ta rutsa ta da tambayoyi."

"Da aka tambayeta sunan jaririn da take goye da shi sai bakinta ya fara rawa ta gaza ba da cikakkiyar amsa. Mai taimakon ta faɗa wa saura cewa ta san yaron da mahaifiyar shi, a takaice ma makotanta ne."

"Daga na sai suka nemi ɗauki, suka kira mahaifiyar jaririn da kuma yan sanda, waɗan da suka kama matar suka tafi da ita caji Ofis domin amsa tambayoyi."

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies