Jita-jita mai karfi na yawatawa tsakanin yan siyasa da al'ummar jihar Kebbi kan zargin yiwuwar tsami tsakanin wasu jiga-jigan yan siyasar jam'iyar APC da sansanin Dan takarar shigaban kasa a jam'iyar APC Bola Ahmad Tinubu bayan ya lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a jam'iyar.
Yunkurin mu na samun cikakken bayani kan gaskiyar lamarin ya gamu da cikas sakamakon nuni da dalilin "hurumi ko izini" kan zancen da wadanda muka tuntuba suka ambato tare da neman a sakaya sunayensu.
Sai dai wani jerin sunayen "Dakarun" da za su taimaka wa Tinubu yin kampen da aiwatar da dubarun lashe zabe a 2023 da wani hadiminsa ya fitar, na neman tabbatar da zargin da ake yi ko akasin haka domin dai babu sunan mutum ko daya daga jihar Kebbi a jerin sunayen da aka fitar.
A cikin jerin sunayen da Igbokwe ya raba a Facebook a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, Gwamnoni, jiga-jigai, da jiga-jigan jam’iyya mai mulki na cikin jihohin da ba su gaza 14 ba, domin su yi kokarin ganin Tinubu ya fito.
Borno: Ali Modu Sheriff, Kashim Shettima, da Babagana Zulum
Kano: Ganduje, Kwankwaso, Shekarau da Tanko Yakassai
Kaduna: El-Rufai da Uba Sani
Yakin neman zabe: Abiodun, Osoba, Amosun da Gbega Daniel
Ekiti: Gwamna Kayode Fayemi, Adebayo, Fayose, Oni, Bamidele, da Adeyeye
Osun: Gwamna Oyetola, Baba Akande, Aregbesola da Omisore
Nasarawa: Governor Sule da Al-Makura
Edo: Adams Oshiomole da Ize-Iyamu
Bauchi: Adamu Adamu da Yakubu Dogara
Gombe: Inuwa Yahaya da Danjuma Goje
Kwara: AbdulRahman zai yi wa Tinubu aiki.
Katsina: Governor Aminu Masari, Hadi Sirika, Dikki Radda da Ibrahim Masari
Zamfara: Governor Bello Matawalle, Marafa, Yerima, Yari dq Shinkafi
Lagos: Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Fashola, Gbajabiamila, Baba Olusi, Annabi Odunmbaku
Igbokwe yace jihar Kwara ce kadai wakilanta duk suka zabi Tinubu
Rubuta ra ayin ka