Type Here to Get Search Results !

Wata mata yar jihar Arewa a Najeriya ta rasu a ranar Arafat a Saudiyya


Hukumar jin dadin alhazai na Jihar Kaduna ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazanta Hajiya Asiya Aminu daga karamar hukumar Zaria a yau Juma'a ranar a Arafat kuma a filin Arafat.

Sanarwar ta fito daga bakin Umar Shehu Zaria kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.

Hakazalika, ita ma hukumar jin dadin alhazai na kasa NAHCON ta tabbatar da rasuwar na Hajiya Asiya Aminu, rahoton Nigerian Tribune.

Ta rasu ne yayin da ta ke barci jim kadan bayan dawowa daga Hawan Arafat a cewar makwabta da ke tanti.

Dr Usman Galadima, Shugaban sashin ayyuka kuma Jagoran likitocin Nigeria ya ce kawo yanzu ba a tabbatar da sanadin rasuwarta ba.

Ya ce an sanar da iyalanta kuma za a yi mata jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Asiya ita ce maniyyaciya ta biyu da ta rasu a kasa mai tsarki a hajjin 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi Jihar Nasarawa ta rasu a makon da ta gabata bayan gajeruwar rashin lafiya an kuma mata jana'iza a Makkah.

Tsayuwan Arafah na cikin farillun aikin hajji.

Maniyyatan Najeriya na cikin miliyoyi da suka yin aikin hajjin na 2022.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies