Wasu ‘yan bindiga sun kai hari motar bas ta KSTA a Katsina, sun kashe direban mota tare da sace fasinjoji (bidiyo)


Wasu ‘yan bindiga a safiyar Lahadi, 24 ga watan Yuli, sun kai hari kan wata motar bas ta kasuwanci mallakar hukumar sufuri ta jihar Katsina (KSTA) sun kashe direban tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. Shafin isyaku.com ya samo.

Manajan Daraktan KSTA, Alhaji Haruna Musa wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Katsina faruwar lamarin, ya bayyana direban mai suna Nasir Yusha’u. 

Alhaji Musa ya bayyana cewa ’yan bindigar da ke wucewa ta hanyar sun harbe direban ne kawai a lokacin da direban ya iso tare da fasinjojin. 

“Ya fito daga Jibia zuwa Katsina, da misalin karfe 11 na safe, sai ya ci karo da ‘yan fashin, nan take direban ya gansu, sai ya yi kokarin tsayawa ya koma, amma abin takaici gare shi, daya daga cikin tayoyin motar ya makale a yashi, haka suka harbe shi har lahira, fasinjojin suka fara gudu." Musa yace. 

“’Yan bindigar sun tattara wayoyin da sauran abubuwan mallakar wasu fasinjojin ne suka bar wurin, madugun motar da ya ba mu labarin abin da ya faru a zahiri ya ce babu daya daga cikin fasinjojin da ‘yan fashin suka sace.

“Tun daga lokacin, ba mu ji wani rahoto ba cewa daya daga cikin fasinjojin da ke cikin motar ya bace yayin harin,” in ji shi.

NAN ta ruwaito cewa hanyar Katsina zuwa Jibia mai nisan Kilomita 46 tana da wuraren binciken jami’an tsaro sama da 15 daban-daban. 

Latsa kasa ka kalli bidiyo

https://mobile.facebook.com/story.php?story_fbid=733631704532101&id=100040173859236&_rdr

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN