Wani dan kasar Italiya ya yi wa wani dan Najeriya duka har lahira a Italiya (hotuna)


Wani dan Najeriya mai shekaru 39 mai suna Alika Ogorchukwu, ya mutu bayan da wani dan kasar Italiya ya lakada masa duka a kan titunan birnin Civitanova Marche da ke lardin Macerata na yankin Marche na kasar Italiya. Shafin isyaku.com ya samo.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Najeriya da ke Italiya ya fitar, ta ce dan kasar Italiyan ne ya kai wa marigayin hari a kan wata hanya mai cike da cunkoson jama'a masu wucewa.

Sanarwar ta kara da cewa Jakadan Najeriya a Italiya, Mfawa Omini Abam, ya yi Allah wadai da kisan. Ya ce a halin yanzu ofishin jakadancin Najeriya yana hada kai da hukumomin Italiya da abin ya shafa don tabbatar da an yi adalci da kuma bayar da taimako ga iyalan mamacin.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN