Wani Alhajin Najeriya ya rasu a birnin Makka na kasar Saudiyya


Allah ya yi wa wani Alhajin Najeriya Wanda ya je aikin Hajjin bana, Alhaji Mamman Nasiru Zungeru rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya. Shafin isyaku.com ya samo.

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Neja, Alhaji Umar Makun Lapai, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli a Minna.

Ya ruwaito cewa:

“Na yi nadamar sanar da rasuwar daya daga cikin Alhazanmu daga jihar Neja, a Makkah. Alhaji Mamman Nasiru Zungeru daga karamar hukumar Wushishi,” sanarwar ta kara da cewa. 

"Mahukuntan kasar Saudiyya ne za su gudanar da Sallar jana'izar, sannan a yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki da Ya jikan marigayi Alhaji Mamman Nasiru Zungeru kuma ya hore masa Aljanat Firdausi, ya kuma baiwa iyalai karfin gwuiwa wajen jure wannan rashi (Amin). 

Sai dai Lapai bai ambaci yanayi ko dalilin rasuwar Alhajin da ya rasu ba. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN