Mahaifiya da 'ya'yanta biyu na daga cikin matafiya da suka kone kurmus a hadarin motar Kaduna (Hotuna)


Wata mata mai suna Fati da ‘ya’yanta mata biyu na daga cikin matafiya 30 da suka mutu a  hatsarin mota  a hanyar Zariya zuwa Kano, Hawan Mai Mashi a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna. Shafin isyaku.com ya samo.

Hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 5.30 na yammacin ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli, 2022, ya yi sanadiyyar jikkata wasu da dama.

Motocin guda uku da hatsarin ya rutsa da su sun tashi da wuta nan take bayan hadarin. Sakamakon haka wasu fasinjoji suka kone kurmus kuma ba a iya gane su. 

Iyalan gidan Gadzama daga jihar Borno, sun bayyana hakan a shafin Facebook. 

"Na yi tsokaci ne kan wannan hatsarin da ya faru a kan hanyar Kaduna, ban sani ba kanwar kawuna ce tare da 'ya'yanta mata, ka huta lafiya Auntie. Babban rashi ga iyalan Gadzama da Wamdeo baki daya," in ji wani Victor Asuka Gadzama.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN