Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana ranakun Alhamis 28 da Juma’a 29 ga Yuli, 2022 a matsayin ranar hutu

FROM : AYODELE AJOGE,  BIRNIN-KEBBI


Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana ranakun Alhamis 28 da Juma’a 29 ga Yuli, 2022 a matsayin ranar hutu. Shafin isyaku.com ya samo.

Hakan na nufin baiwa ma’aikatan gwamnati damar ko dai su samu ko kuma sabunta katin zabe na dindindin.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayar da wannan izinin ne a ranar Larabar da ta gabata, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan, Alhaji Safiyanu Garba Bena, wadda aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.

A cewar sanarwar, hakan ya zama dole domin karfafa gwiwar al’ummar jihar baki daya a ci gaba da gudanar da rijistar masu kada kuri’a da za a kammala a ranar Asabar kamar yadda INEC ta bayyana.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da wannan hutun na kwanaki biyu don gudanar da ayyukansu na al’umma, don kada a tauye hakkinsu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN