Uwargida ta banka wa maigida wuta har Lahira daga bisani ta kashe kanta, duba dalili


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya ce Ifeoluwa Bamidele, matar da ta bankawa mijinta mai suna Bolu wuta a gidansu da ke kauyen Koka, a karamar hukumar Obokun ta jihar Osun a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, ta kashe kanta. Shafin isyaku.com. ya samo.

A zantawarsa da LIB, SP Opalola ya ce Ifeoluwa ta kashe kanta ne a daren Alhamis, 21 ga watan Yuli da misalin karfe 7 na dare.

Kakakin ‘yan sandan ya ce kokarin jin ta bakin Ifeoluwa da ta fara buya a jihar Ekiti ya haifar da sakamako a ranar Alhamis bayan da ta samu wata kungiya mai zaman kanta ta shiga tsakani. 

Opalola ta ce Ifeoluwa ta bayyana cewa tana Aramokoko kuma zai yi mata wahala ta samu sufuri zuwa Osogbo. SP Opalola ta ce daga nan ta umarci wasu ma’aikata da su je su dauke ta daga inda take. 

''Lokacin da suka dauko ta ne suka ga ta na wasa. Suka tambaye ta me ya faru. Ta furta cewa ta sha wani abu mai guba kafin ta bar Ekiti. Mun garzaya da ita asibitin WesleyGate. Sai da suka yi iya kokarinsu don ta yi amai duk abin. Daga baya sun gano cewa ta dade da Shan guba kuma ya lalata mata cikinta. Haka ta mutu''

Rahotanni sun ce Ifeoluwa ta kona Bolu bayan da ta gano ya sami wani yaro da wata mata daban. Aurensu bai cika shekara daya ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN