An kama wasu mutane takwas da ake zargi da laifin fille kan dan Majalisa- Gwamna Soludo


Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya ce an kama wasu mutane takwas da ake zargi da laifin fille kan dan Majalisar dokokin Anambra, Okechukwu Okoye mai shekaru 44. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

An yi garkuwa da dan Majalisar mai wakiltar mazabar Aguata 2 a Majalisar dokokin jihar Anambra a watan Mayun bana tare da wani mutum daya a cikin motarsa ​​Toyota Sienna. A ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, an gano kan sa a Nnobi, cikin karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra, inda aka rataye shi kuma aka ajiye gawarsa.

Da yake jawabi a wajen bikin jana’izar dan Majalisar a Cocin St. Patrick’s Catholic Church, Isuofia, karamar hukumar Aguata a jihar a yau, Gwamna Soludo ya ce Gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an gurfanar da masu laifin da suke da hannu a kashe dan Majalisar a gaban kotu. 

Gwamnan ya jajantawa iyalan dan Majalisar da ‘yan Majalisar dokokin jihar sannan ya bukaci al’ummar jihar da su kara ba Gwamnatin jihar goyon baya wajen yaki da masu aikata laifuka.

Wadannan mutane ba ’yan bindiga ne da ba a san su ba. Suna zaune a cikin mutanenmu, wasu daga cikinsu suna da iyalai kuma suna aiki daga al'ummomi daban-daban. Muna bukatar ku taimaka mana ku zakulo su domin su fuskanci shari'a'' Gwamna Soludo.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN