INEC ta cire dan Abacha a matsayin dan takarar Gwamna na PDP a Kano


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da Sadiq Wali a matsayin dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

Rikicin da ya barke a jam’iyyar adawa ta Kano ya kai ga gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar, wanda ya haifar da ‘ya’yan tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali da na marigayi tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar 30 ga watan Yuni, Kwamishinan Zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu ya ce hukumar ta sanya ido kan zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar karkashin Shehu Wada Sagagi wanda ya samar da Mohammed Abacha a matsayin dan takarar Gwamna.

Sai dai babban jerin sunayen ‘yan takarar Gwamna da aka raba a ranar Juma’a 22 ga watan Yuli a ofisoshin INEC na jihar, ya nuna cewa an amince da sunan Wali da na mataimakinsa Yusuf Dambatta a matsayin ‘yan takarar PDP a jihar. 

Da yake tsokaci kan haka, jami’in hulda da jama’a na INEC na jihar Kano, Ahmad Adam Maulud, ya ce hukumar a matakin jiha ce kawai ta mika sakamakon zaben fidda gwani da ta sa ido a hedikwatar ta kasa.

Daily trust ta ruwaito cewa Maulud ya ce abin da aka manna a bango a ranar Juma’a shi ne abin da aka dawo da shi daga hedikwatar kasar.

Yace; 

“Mun aika abin da muka yi zuwa hedikwatarmu ta kasa kuma abin da muka lika a yau (Juma’a) ya fito daga gare su kai tsaye.

"Duk wanda ke son neman karin haske ya tuntubi kungiyar jam'iyyarsa ta kasa don samun bayanai."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN