Takarar Tinubu-Shettima: Jami’an DSS sun ankarar da Buhari abin da suka hango


Matsayar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dauka na tsaida Musulmi a matsayin abokin takara a zaben shugaban kasa, zai iya jawo rigima a kasa. 

Rahoton da Leadership ta fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa hukumar DSS ta rubutawa shugaban kasa takarda a game da shirin da APC ta ke yi a 2023.

Bayanan tsaro na sirri da hukumar farin kaya na DSS ta aikawa Mai girma shugaban kasa ya nuna daukar Musulmi da Musulmi zai iya haifar da rikicin addini.

DSS ta gabatar da binciken, kuma ta damka rahoto ga Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Janar Babagana Monguno mai ritaya domin a dauki mataki.

DSS ta nunawa Janar Babagana Monguno cewa ya kamata Bola Tinubu ya duba halin tsaro da kasa za ta samu kan ta, kafin ya dauko abokin takararsa a APC.

Jaridar nan ta Peoples Gazette ta samu ganin takardar bayan ta shiga ofishin Babagana Monguno.

Wata majiya ta shaida cewa shugaban NSA ya duba rahoton, ta kuma sa shi a jerin abubuwan da zai tattatuna da Mai girma shugaban Najeriya idan sun zauna.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN