Wani dan kasar Indiya mai shekaru 55 ya fille kan matarsa, mai shekara 45, bayan da ya zarge ta da yin lalata da wani, sakamakon haka ya fille kanta, daga bisani kuma ya yi tattaki a kalla kilomita 12 zuwa ofishin 'yan sanda dauke da kan matar. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.
Lamarin ya faru ne a Chandrasekharpur a gundumar Dhenkanal ta Odisha da sanyin safiyar Juma'a 15 ga watan Yuli.
Yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake tafiya rike da kan matar da ya yanke zuwa ofishin ‘yan sanda na Gonida da ke gundumar Dhenkanal.
Mutumin mai suna Nakaphodi Majhi, dan kauyen Chandrasekharpur da ke karkashin ofishin ‘yan sanda na Gondia ya auri matarsa Sachala Majhi tsawon shekaru 25. Suna da 'ya'ya biyu da suke zama a wajen Æ™auyen.
‘Yan sanda sun ce Nakaphodi na zargin Sachala da cin amanarsa kuma yakan yi fada da ita. Bayan da aka samu sabani tsakanin ma'auratan, sun shafe lokaci mai tsawo suna rigima da juna.
Da misalin karfe 3:30 na safe zuwa 4 na asubahin ranar Juma’a, Nakaphodi ya kashe ta ta hanyar yanka mata makogwaro da makami mai kaifi (Katuri). Sannan ya sare mata kai ya isa ofishin ‘yan sanda na Gondia da yankakken kanta ya mika kansa a ofishin Yan sanda, in ji rahotun ‘yan sandan.