An kashe wata mata bayan an caka mata wuka a dakin Otal a Sokoto sakamakon gardamar N1000


An kama wani mutum bisa zargin kashe wata mata mai zaman kanta a Kwanawa, cikin karamar hukumar Dange/Shuni a jihar Sokoto. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

An tattaro cewa abokin cinikin ya caka wa matar wuka har lahira a lokacin fadan da ya barke tsakanin su bayan ta ki amincewa da N1000 da ya ba ta bayan sun aikata lalata. 

Majiyoyi a yankin sun shaida wa jaridar Punch  cewa, wanda aka kashen tana zaune ne a daya daga cikin gidajen karuwai da ke yankin da aka sansu da duk wani nau’in haramun. 

Wata majiya ta ce karar da makwabtan da ke kusa da otal din da masu wucewa suka ji ne ya ja hankalin mutanen da suka kama wanda ake zargin a lokacin da ya yi yunkurin guduwa bayan ya gano cewa wanda ya caka wa wuka ta mutu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Sanusi Abubakar, wanda ya tabbatar wa jaridar Punch faruwar lamarin, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi mai bincike ne da ya ziyarci Jihar Sakkwato domin gudanar da bincike.

Abubakar ya ce wanda ake zargin ya yanke shawarar kwana tare da karuwar amma ya ce matsalar ta fara ne lokacin da wanda ake zargin ya biya wanda aka kashe Naira 1,000.

Jami’in PPRO ya ce wanda abin ya shafa ta ki amincewa da kudin, wanda hakan ya haifar da fada a tsakaninsu.

A cewar kakakin, wanda ake zargin ya fito da wata wuka ya yi amfani da shi wajen daba mata bayan ya rinjaye ta.

Abubakar ya kara da cewa an mayar da shari’ar zuwa sashin kisan kai na rundunar domin gudanar da bincike mai kyau. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN