Rikici ga Tinubu, Atiku yayin da wani Limamin Arewa ya yi wa wani dan takarar shugaban kasa kamfen a Hudubar Sallar Idi


Rahotanni sun bayyana cewa, babban limamin Masallacin Juma’a na Daawah Kano, Sheikh Muhammad Aminuddeen ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) Rabi’u Kwankwaso da ya ci gaba da burinsa da himma.

Da yake gabatar da wa'azin sallar Eid-El-Kabir ga dubban Masallata ciki har da Kwankwaso a ranar Asabar 9 ga watan Yuli, Limamin ya ce tsohon Gwamnan jihar Kano "yana da dukkan halayen da zai jagoranci Najeriya kuma ya zarce 'yan takarar shugaban kasa na APC da PDP."

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sheikh Aminuddeen ya lura cewa Sanata Kwankwaso “yana da matukar kishin ci gaban Najeriya”.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya kubutar da Nijeriya daga kalubalen tsaro da ake fama da shi, ya kuma yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari jagora ya jagoranci kasar nan cikin nasara.

Sallar ta kuma samu halartar dan takarar Gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano Abba Kabir Yusuf da abokin takararsa Kwamared Aminu Abdussalam da sauran manyan baki.

Legit.ng ta tattaro cewa babban limamin dan gidan marigayi Sheikh Aminuddeen Abubakar ne, shahararren Malamin addinin Musulunci a Kano kuma ya kafa kungiyar Daawah Group of Nigeria.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN