Wani matashi dan kishin kasar Zuru da ake kira da suna Yahuza Dada.Ya yi kira ga Gwamnatin Jahar Kebbi da su sa baki don a cigaba da gyaran hanyar Koko zuwa Dabai na kasar Zuru kasancewar an fara gyaran hanyar daga baya aiki ya tsaya.
Al'ummar Zuru na wahala da yawa akan hanyar saboda lalacewar ta kusan kullum motoci suna lalacewa akan hanyar lamari da ke haifar da wahalar da allumma ke sha kafin su isa garin Zuru ko kuma idan aka taso daga Zuru zuwa koko. Mutane na shan wahala kusan kullum kuma itace kadai hanyar da ake bi kowa ne lokaci, bayan haka kuma idan an dauko marar Lafiya daga Zuru zuwa Asibitin Birnin kebbi haka al'umma ke shan wahala da galabaita kafin su isa koko.
Sannan yanzu hanyar ababen hawa sun karu, yawancin wayanda ke zuwa Sokoto sun koma suna bin hanyar saboda matsalar tsaro dake addabar mutane a kan hanyar zuwa Daki takwas dake Zamfara.
Tuni motoci na samun hatsari a kwalbatin dake da hanyar ruwa wa yanda ruwa ya fara cinye gefen su har sun fara yankewa a gefe wanda idan ba a dauki matakin Gyaran su ba cikin gaggawa zasu iya yankewa.
Yahuza ya yi kira ga Gwamnatin jahar Kebbi da na kusa da Gwamna su taimaka domin magance wannan babbar matsalar dake damun al'ummar Masarautar Zuru.
Kazalika Yahuza ya kara da cewa an jima ana kai kukan jama'ar Masarautar Zuru dangane da lamarin hanyar zuwa ga Gwamnatin jaha. Amma har yanzu ba za mu gaji ba da kai korafi domin bamu da hanyar da ta wuce muna wannan hanyar a yankin Zuru baki daya.
Daga Yahuza Dada Zuru
![]() |
Yahuza Dada Zuru |
![]() |
Manyan ramu da ke haifar da hadurran motoci |
![]() |
Yadda iyalan matafiya ke Shan wahala sakamakon lalacewar mota a hanyar Koko-Dabai |
Rubuta ra ayin ka