An kama wani mai garkuwa da mutane bisa zargin kashe tsoho mai shekaru 80 duk da karbar kudin fansa


An kama wani mai garkuwa da mutane da ake zargin ya kashe tsohuwa mai shekaru 80 duk da karbar kudin fansa an kama shi a jihar Kwara. Shafin isyaku.com ya samo.

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Kwara sun kama wani da ake zargin dan kungiyar masu garkuwa da mutane uku ne mai suna Boodoo Musa Alhaji da laifin yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

‘Yan kungiyar sun yi garkuwa da wani dattijo mai shekaru tamanin mai suna Alhaji Abba a garin Eruwa na jihar Oyo, inda suka karbi kudin fansa, inda daga bisani suka kashe shi.

Da yake tabbatar da kama shi ga manema labarai, jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC na jihar Kwara, Olasunkanmi Ayeni, ya ce wanda ake zargin wanda tsohon mai laifi ne ya aikata laifin a Eruwa, Oyo yayin da aka kama shi a unguwar Banni da ke karamar hukumar Kaiama. Jihar Kwara a karshen mako.

Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya musanta ikirarin cewa shi mai garkuwa da mutane ne. A cewar sa shi manomi ne.

“An kama ni ne saboda wanda aka kashe ya shaida wa wani Alhaji Isiaka, dan kungiyar ’yan banga a yankin kafin faruwar lamarin cewa a kama ni idan wani abu ya same shi,” inji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN