Kotu ta umurci mata da ta mayar da katifar mijin da suka rabu, duba dalili

Kotu ta umurci mace da ta mayar da katifar mijin da suka rabu


Wata kotun shari’a da ke Kaduna a ranar Litinin ta umurci wata mata mai neman saki, Halima Ahmad da ta mayar da katifar tsohuwar matar mijinta, Suleiman Atiku. Shafin isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa a baya Atiku, jami’in gidan gyara hali ne ya nemi a ba shi katifarsa, kafin ya amince da bukatar sakin ta.

Halima wacce ke zaune a unguwar Badarawa a Kaduna, a watan Aprilu 2p22 ta shigar da karar neman Kotun Sharia da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna da cewa Kotu ta kashe aurensu da mijinta.

Alkalin Kotun ya umarci mijin ya baiwa Halima Naira 20,000 domin ta samu damar siyan sabuwar katifa.

Alkalin ya kuma umurci Mijin da ya biya Halima Naira 80,000, domin ta biya bashin da ta ci a lokacin aurensu.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yuli, saboda yanke hukunci kan bukatar saki.

Tun da farko dai, wacce ake kara, wadda ba ta bayyana dalilin neman a raba auren ta ba, ta shaida wa kotun cewa a shirye ta ke ta mayar wa Atiku kudin aurenta.

Atiku ya shaidawa kotu cewa katifar na matarsa ​​ta farko ce

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN