Wamakko ya magantu ya aike wani muhimmin bukata ga yan siyasa



Sanata Aliyu Wamakko (APC-Sokoto ta Arewa) ya bukaci ‘yan siyasa da su gudanar da siyasa ba tare da gaba ba a daidai lokacin da zaben 2023 ke gabatowa. Kafar labarai mai zaman kanta na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan sabbin kafafen yada labarai Malam Bashar Abubakar ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

“A ci gaban babban zabe mai zuwa, mu a matsayinmu na ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a tsarin dimokuradiyyar kasar nan, dole ne mu bi ka’ida tare da tabbatar cewa mun kauce wa ayyukan da ba su dace ba.

Abubakar ya bayyana cewa Wamakko ya bayar da wannan bayani ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga kungiyoyi daban-daban da suka kai masa ziyarar Sallah a Sokoto.

Ya kara da cewa Wamakko ya bayyana fatansa cewa nan ba da jimawa ba kalubalen tsaro da kasar nan ke fama da shi za su zama tarihi, ya kuma gode wa Allah da ya ba duk wanda ya shaida wannan bikin Sallah.

Ya yi addu’ar Allah ya kawo wa ‘yan Najeriya taimako don shawo kan matsalolin tattalin arziki da ake ciki a yanzu, ya kuma bukaci masu imani da su kara yin addu’o’in neman taimakon Allah a duk kalubalen rayuwa.

Ya godewa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar kan “juriya da karewa da kuma addu’o’in da suka nuna na samun nasarar jam’iyyar a dukkan matakai musamman ganin babban zabe na gabatowa”.

Wamakko ya bukaci magoya bayansa da su tabbatar sun samu katin zabe na dindindin domin shi ne kawai makamin da ake bukata wajen zaben shugabanni masu nagarta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN