Magoya bayan PDP a jihar Borno sun fatattaki shugaban jam’iyyar, sun hana shi shiga sakatariyarta


Fusatattun mambobin PDP a ranar Lahadi, sun mamaye sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri don hana dakataccen shugaban jam’iyyar reshen jihar Borno, Alhaji Zanna Gadama, shiga ofishinsa don gudanar da wani taro da jawabi ga manema labarai.

Legit.ng ta ruwaito cewa Gadama ya gayyaci manema labarai don su nadi taron masu ruwa da tsaki da ya kira bayan dakatar da shi da wasu jami’an jam’iyyar suka yi kwanaki da suke wuce, Vanguard ta rahoto.

Sai dai kuma, da shigarsa sakatariyar ya tarar da magoya bayan jam’iyyar wadanda suka mamaye dakin taron inda suka bukaci ya fice daga harabar wajen.

Magoya bayan jam’iyyar wadanda suka yi tofin Allah tsine ga dakataccen shugaban sun zarge shi da wawure kudaden jam’iyyar tsakanin 2019 zuwa yau, jaridar Leadership ta rahoto.

Sun kuma sha alwashin cewa idan ba a tsige shi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a Borno ba daga jam’iyyar har dan takararta shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ba za su samu kuri’unsu ba.

Hakazalika, sun zargin shugaban jam’iyyar da hada kai da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar don kifar da jam’iyyar a duk shekarun zabe.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN