Wasu fusatattun mutane sun kona wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a karamar hukumar Aba ta jihar Abia. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro.
An tattaro cewa mutanen suna cikin masu aikata laifukan da suka addabi ma’aikatan Point of Sale (POS), ‘yan kasuwa, mazauna Abayi, kan titin Aba-Owerri, Afor-Ule, Umuimo da kuma titin Kamalu a kan titin Osisioma na Aba.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an kona wadanda ake zargin sun yi fashi ne a wurare daban-daban a ranar Lahadi 3 ga watan Yuli.
An kona guda daya daura da ginin UBA, yayin da aka kone wasu a mahadar bankin Union da kuma Star Paper Mill da ke kan titin Kamalu da ke kan titin Aba/Owerri.
Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Vanguard cewa wasu fusatattun matasa ne suka kama mutanen bayan da suka yi wa wani ma’aikacin PoS fashi da wasu shaguna a yankin.
Rubuta ra ayin ka