Type Here to Get Search Results !

Zarge-zarge sun kunno kai yayin da aka ce gwamnatin Buhari ta kori mukaddashin AGF na Najeriya


Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar na nuni da cewa an tsige mukaddashin Akanta-Janar na kasa Chukwuyere N. Anamekwe daga ofishin sa. 

Jaridar ta bayyana cewa an maye gurbin Anamekwe da Okolieaboh Ezeoke Sylvis, wanda ya taba rike mukamin tsohon darakta na asusun bai daya na Treasury Single Account (TSA). 

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa gwamnatin tarayya na neman sabon AGF. Wanda ya maye gurbin Anamekwe tsohon darakta ne na TSA

A bisa haka ne, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF), Folasade Yemi-Esan ta fitar da wata sanarwa ga sakatarorin dindindin na mika mata cikakkun bayanai na daraktocin da suka cancanta a mataki na 17 zuwa gare ta kafin karfe 4:00 na yammacin Laraba 6 ga watan Yuli. 

Da yake bayyana cancantar matakin 17 na jami'an da suka cancanci shiga ofishin, wani bangare na bayanin ya karanta: 

“Wadanda suka samu mukamin Babban Darakta (Grade 17) a ranar 1 ga Janairu, 2020, kuma ba su yi ritaya daga aikin ba kafin ranar 31 ga Disamba, 2024, sun cancanci shiga cikin tsarin zaben yayin da jami’an da ke fuskantar shari’ar ladabtarwa ." 

Dalilin maye gurbin 

An tattaro cewa korar Anamekwe ta biyo bayan zargin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ke bincikensa. 

Haka kuma, an bayyana cewa gwamnati ba ta ji dadin ikirarinsa na cewa ta na karbar bashi domin biyan albashi ba. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies