Type Here to Get Search Results !

Kotu ta yanke hukuncin jefe wata mata da duwatsu har ta mutu


Wata babbar kotu ta yanke wa wata ‘yar kasar Sudan hukuncin kisa ta hanyar jifa da duwatsu sakamakon laifin aikata zina. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

‘Yan sanda a jihar White Nile da ke Sudan sun kama Maryam Alsyed Tiyrab, ‘yar shekara 20 a watan da ya gabata, kafin a yanke mata hukunci a kotun hukunta manyan laifuka ta Kosti a ranar 26 ga watan Yuni, in ji jaridar Mail Online.

Jaridar ta ce Ms Tiyrab ta rabu da mijinta kuma ta koma gidan 'yan uwanta, kafin daga bisani 'yan sanda su yi mata tambayoyi sakamakon daukar ciki ba tare da aure ba.

Sai dai ta daukaka kara kan hukuncin da fatan babbar kotun ta yi watsi da hukuncin.

Rahotanni sun ce an hana Ms Tiyrab samun wakilcin Lauyoyi, kuma an fara shari’arta ne ba tare da samun takardun korafi daga ‘yan sanda ba, wanda kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka ce ba a bi ka’ida ba.

A tsarin shari'ar Musulunci, laifukan Hudud da ake aiwatarwa a Sudan suna dauke da hukunci kamar yanke hannu da ƙafafu, bulala, da kuma kisa.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies