Da dumi-dumi: IGP Baba ya haramta amfani da duk wata lambar SPY ta ‘yan sanda kan ababen hawa a Najeriya


Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ya haramta amfani da lambar mota na ‘yan sanda SPY a fadin Najeriya. 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce umarnin ya shafi masu ababen hawa a fadin jihohin tarayyar kasar nan, inji rahoton The Cable . 

Baba ya bayyana cewa hakan ba tare da la’akari da ko an ba da izinin lambar ba, ko a’a, saboda an soke duk wasu izini har abada. 

Ya ce an sanar da wannan umarnin ne saboda bukatar kawo karshen “ci gaba da yin watsi da ka’idojin hanya da sauran dokoki da ke jagorantar yin amfani da hanyoyi da mutanen da ke boye a karkashin gata na lambar ‘yan sanda ta SPY.” 

Wani bangare na umarnin IGP na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar CSP Olumiyiwa Adejobi ya fitar, ya ce: 

Saboda haka IGP din ya umurci jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da ke da alaka da VIPs masu amfani da lambar SPY su tabbatar da bin wannan umarni cikin gaggawa ko kuma a kama su da laifin karya wannan umarni. 

“A halin da ake ciki, IGP ya umurci kwamishinonin ‘yan sanda (CPs) na jihohi talatin da shida (36) na tarayya da babban birnin tarayya, da kuma mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda (AIGs) da su ba da cikakken tasiri kan umarnin kamar yadda yake a sama. 

IGP na musamman ya umurci AIG da CPs da su tabbatar da cewa an kwace duk wata lambar SPY da ake amfani da su a yanzu amma bai kamata a kama masu irin wadannan motocin ba sai dai idan ‘yan sanda ne ko jami’an tsaron da ke aikin rakiya. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN