Bidiyon mai digirin digir yana tallar kwai, ya nemi aiki sau 5000 bai samu ba


Duk da mallakar digirin digir da yayi tare da sauran kwalayen shaida karatuttuka, wani 'dan kasar Kenya mai suna Dennis ya rasa aikin yi.

Bayan kammala digirinsa na farko a 2013, Dennis ya samu aiki amma ya yanke shawarar komawa karatu kuma yayi nasarar kammala digirinsa na biyu a 2018.

Tun bayan da ya kammala digirinsa na biyu kuma ya tara kyawawan satifiket masu amfani, matashin wanda ke da shekaru 39 bai samu wani aikin ba.

A yayin bada labarinsa a wani bidiyo mai taba zuciya da Afrimax English ta saka a YouTube, Deniis yace ya nemi aiki har sau 5000 amma bai taba samun ko daya ba

Domin samu na rufin asiri, Dennis wanda ya karanci fannin tattalin arziki da kasuwanci ya koma siya da kwai danye, dafaffe da miyar tumatir a titin Nairobi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN