An yi wa matar marigayi Abba Kyari nadin mukamin gargajiya, Sarki ya yi karin bayani


Sarkin Jama’are, Alhaji Nuhu Wabi III, ya yi wa matar tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa (CoS) marigayi Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu a matsayin ”Gimbiyar farko” na Jama’are. Shafin isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa da yake jawabi a wajen bikin a fadarsa ranar Lahadin da ta gabata, Sarkin ya bayyana ta a matsayin ‘yar Jama’are ta gaskiya wacce ta yi kokari wajen ci gaban Masarautar baki daya.

Marigayi Kyari ya fito daga Borno, amma matarsa, Hauwa, Nee (Gidado) ta fito daga garin Jama'are a karamar hukumar Jama'are a jihar Bauchi.

“Aikin gargajiya na Gimbiya, diyar Sarki ce kuma mai alaka tsakanin Sarki da mata, wadanda ba su da damar kaiwa kai-tsaye ga Sarki a cikin al’amuran gargajiya.

“Da wannan nadin, matan Jama’are yanzu suna da wakiliya a Majalisar Masarautar, yanzu ana iya jin muryoyinsu karara ta wajen "Gimbiya". 

"Na yi amanna cewa yanzu ina da 'yar Masarautar ta gaske a Majalisar," in ji Sarki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN