Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Sokoto, ta ce za ta yi gwanjon motocin da aka kama da masu motocin basu zo suka karba ba. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.
NAN ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mista Salisu Tureta, kuma ya bayyanawa manema labarai ranar Alhamis a Sokoto.
Ya ce gwanjon zai shafi motocin da suka kade masu su basu zo suka karba ba a hannun hukumar.
PRO ya ce masu irin wadannan motocin suna da kwanaki biyu domin su karbi motocin su.
“Hukumar FRSC tana sanar da jama’a aniyar ta na yin gwanjon ababen hawa da babura da suka dade a cikin rajistar tsare su.
Tureta ya kara da cewa, "Rundunar ta na baiwa jama'a sanarwar sa'o'i 48 ga wadanda ke son karbar motocinsu da babura su zo da ingantattun takardun motocinsu tare da biyan kudaden da ake bukata," in ji Tureta.