Kar ku roke shi: Sabon rikici ya barke yayin da dan PDP BoT ya bayyana abinda ya kamata Jam'iyyar ta yiwa Gwamna Wike


Adamu Maina Waziri, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya caccaki matakin da jam’iyyar ta dauka na rokon gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas kan zaben gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a kansa.

Legit.ng ta wallafa cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta fada cikin yakin sanyi tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya bayyana Okowa a matsayin abokin takararsa.

A kokarin warware rikicin, shugaban jam’iyyar PDP BoT, Walid Jibrin, a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli, ya ce jam’iyyar za ta aika da tawaga da za ta hada da Atiku, Okowa, kwamitin ayyuka na kasa da kuma mambobin BoT domin sulhuntawa da Wike.

Kada mu roki Wike, inji Waziri

Da yake mayar da martani, Waziri, wanda tsohon Ministan harkokin ‘yan sanda ne ya caccaki ra’ayin, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin sanin ya kamata, inji rahoton Daily Trust.

Yace:

"Wike yana da matsananciyar damuwa kuma yana buƙatar lokaci don samun jaje game da abin da ya faru. Na yarda da sulhu amma inda muka rabu shi ne batun tura waccan tawaga mai karfi ta durkusa masa.

“Duk shawarar da jam’iyyar za ta yanke, ya kamata duk ‘yan uwa masu biyayya su bi, mu ajiye duk wani abu da ya faru a lokacin zabukan fidda gwani, mu ci gaba, jam’iyyar ta fi maslahar mu baki daya.

"Wike ya ce ba zai yi takara da kowa ba saboda haka dole ne mu nemo wanda zai yi aiki tare da dan takarar shugaban kasa."

Waziri ya kuma karyata jita-jitar da ake yadawa cewa Atiku ya aike shi domin tattaunawa da Wike a kasar Turkiyya.

"Atiku bai aike ni ko'ina ba amma tabbas na je Istanbul Turkiyya don hutuna a ranar Juma'ar da ta gabata kuma mun hadu a wani otal a kwatsam, shi ke nan," in ji shi.

Ayu na cikin matsala yayin da sansanin Wike ya ba da yanayi mai tsauri don marawa Atiku baya

A halin da ake ciki kuma, sansanin Gwamna Wike ya yi kira ga Iyorchia Ayu da ya bar kujerar sa kafin su marawa Atiku takarar shugaban kasa.

Ana zargin ‘yan dabarar Wike na dagewa cewa Atiku ya cika alkawarin farko da suka yi cewa da zarar dan takarar shugaban kasa na PDP ya fito daga arewa, dan kudu zai karbi mukamin shugaban jam’iyyar na kasa.

Sai dai martanin da sansanin Atiku ya bayar shi ne, Ayu na iya ficewa ne kawai bayan zaben 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN