A ranar 5 ga watan Yuli ne jami’an ‘yan sandan jihar Ogun suka kama wasu mutum biyun Adetunji Alagbe da Opeyemi Ogunlokun bisa laifin satar ragon Sallah na wani Sodiq Abolore. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
An kama wadanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da Sodiq Abolore ya kai hedikwatar ofishin Yan sanda na Ogijo, inda ya yi karar cewa a lokacin da yake barci a gidansa da misalin karfe 3 na dare, sai ya ji hayaniya da ba a saba ji ba a harabar gidan nasa, wanda hakan ya sa ya leko ta tagar, sai kawai ya gano cewa an ciro kofar karfen da ya yi amfani da shi wajen toshe kofar da ya ajiye ragon Sallah.
Abolore ya ce hakan ne ya sa ya fito ya gano ragon sa na Sallah da ya saya a kan kudi #120,000 ba ya nan.
Ya ci gaba da cewa, da ya zagaya, sai ya ga wasu mutane uku suna tursasa ragon nasa cikin wata rumfar mota ta Mazda, wanda hakan ya sa ya yi ta kururuwa, kuma aka yi wa ‘yan sanda kira na damuwa
An kori mutanen uku, kuma an kama biyu daga cikinsu, yayin da daya ya tsere.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce an gano ragon, kuma an kai mutanen biyu gidan yari.