An cafke wata mata da ke sayar da gawaki daga gidan ajiye gawa da jana'iza, yadda lamarin ke faruwa


Wata ‘yar kasar Amurka tana fuskantar tuhume-tuhume kan sayar da gawawwaki domin samun kudi kudi da kuma bai wa iyalai da ke bakin ciki tokar karya da ta yi ikirarin cewa na ‘yan uwansu ne bayan an kone gawakin.

Ana zargin Megan Hess ne da mika wa iyalai Kasko masu cike da toka na karya don boye zambar nata.

Matar mai shekaru 45, wacce a baya ta musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake mata, a karshe ta amince da gaskiyar lamarin yayin da aka shigar da karar ta gaban kotu a farkon makon nan.

Wani bincike da FBI ta gudanar ya gano cewa Hess ta yi jabun fom din ba da agaji da dama a gidan jana'izarta na Sunset Mesa da ke garin Montrose, kafin ta sayar da kawuna daban-daban, hannaye, kashin baya da kafafun wasu gawaki ga masu binciken Likitanci tare da cirewa da sayar da hakoran zinare na wasu daga cikin gawakin.

Hess, wacce ake zargi da girbin jiki daga 2010 zuwa 2018 tare da mahaifiyarta Shirley Koch, an kuma yi imanin cewa ta yi amfani da dubunnan daloli da ta samu daga wannan harkalla don yin balaguro zuwa Walt Disney World.

Tana cajin $1,000 (£ 8,400) a ko wace gawa da za ta kona, tana kuma yiwa iyalai matalauta kunar gawa kyauta, sai ta yi amfani da gawakinsu domin ribarta.

Ana kuma zargin uwar da diyar da jigilar gawarwakin wadanda aka yi musu gwajin cuta ko kuma suka mutu daga cututtuka irin su Hepatitis B da C da HIV, duk a lokacin da suke fadawa masu saye cewa ragowar ba su da wata cuta.

Kafin amsa laifin ta na baya-bayan nan, Hess ta gurfana a gaban kotu a makonni masu zuwa, yayin da Koch - wanda a baya ta ki amsa laifinta, za ta fuskanci Kotu ranar 12 ga watan Yuli.

Hess na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN