Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Masu Yawa Sun Koma ADC a Sokoto


Dubban magoya bayan ne a ranar Alhamis suka fito domin tarbar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, Dumebi Kachikwu a Sokoto.

Kachikwu da wasu manyan shugabannin jam'iyyar na ADC sun dira Sokoto ne domin kaddamar da sabuwar sakatariyar jam'iyyar tare da karbar daruruwan sabbin mamabobi da suka baro jam'iyyar APC zuwa ADC.

Dan takarar shugaban kasa jam'iyyar na ADC a zaben 2023 ya tarbi jiga-jigan jam'iyyar APC fiye da 120 da suka fice suka dawo ADC, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kachikwu ya shaida wa wadanda suka sauya shekan cewa ADC ta yi imani da kasa daya dunkulalliya, cigaban yan Najeriya baki daya, girmama doka da kauna sune abubuwan da suka hada kan yan Najeriya.

Ba za mu bawa Sakkwatawa kunya ba - Kachikwu

Ya ce sabuwar sakatariyar za ta zama alama na fatan samun alheri a nan gaba, yana mai cewa ADC ba za ta bawa mutanen Sokoto kunya ba.

Kachikwu ya fada wa magoya bayan jam'iyyar su rungumi ADC a matsayin jam'iyya na dukkan yan Najeriya, a yayin da ya basu tabbacin cewa ba bu wariya a tsakanin mambobi a dukkan lokuta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN