Yan sandan gundumar Bungoma na kasar Kenya, sun kama wata Mata yar shekara 25 mai suna Ms Ng’etich bayan wani mutum mai suna Moses Nabibya ya mutu a dakin Otal daya tare da ita. Shafin labarai ya yanar gizo isyaku.com ya ruwaito.
Mr Nabibya, shi ne tsohon Sakataren gudanarwa na Ford Kenya a Bungoma kafin mutuwarsa. An Sami gawarsa a gidan baki na Misikhu a Webuye ranar Alhamis 30 ga watan Yuni.
Kwamandan Yansandan Webuye na gabas Martha, ya ce an kama matar ne saboda tana tare da Mr. Nabibya iya lokacin zamansa a dakin Otal din kafin mutuwarsa.
Rahotanni sun ce Mr. Nabibya ya shigo Otal din ne tare da matar da karfe 11 na dare ranar Alhamis. Ya ce sai dai da safe misalin karfe 5 sai matar ta ruga wajen Manajan Otal ta nemi taimako bayan mutumin ya koka cewa yana fama da ciwon kirji da alamar hawan jini.
Ya ce sai dai kafin matar da Manaja su isa dakin Otal sun tarar ya riga ya mutu . Yansanda na ci gaba da bincike bayan sun kma matar da yake tare da ita a cikin dakin Otal kafin mutuwarsa.