Kiran da ake yi wa matasa na shiga siyasa zai yi aiki a zaben 2023. Jaridar nan ta Punch ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar a makon nan.
A wannan rahoto, an tattaro sunayen matasan taurari da suka amsa wannan kira, suka shiga siyasa, har suka samun tikitin shiga takara a zabe mai zuwa.
A nan za a samu taurari biyar da za a gwabza da su wajen neman kujerar siyasa a 2023:
1. Funke Akindele
A 2023, ‘Yar wasar Nollywood kuma mai hada fina-finai, Miss Funke Akindele za ta tsaya takarar kujerar matamakiyar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar PDP.
Dr. Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor ya dauki ‘yar wasar a matsayin abokiyar takararsa. Tun 1999 har yau, PDP ba ta taba mulkin Legas ba.
2. Banky W
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakin nan kuma ‘Dan fim, Bankole Wellington wanda aka fi sani da Banky W ya sake tsayawa takara a 2023, ya na neman kujerar majalisar tarayya a PDP.
Idan Banky W ya yi nasara a zaben, zai wakilci mazabar Eti Osa a majalisar wakilan tarayya.
3. Desmond Elliot
Yanzu haka Desmond Elliot ne yake rike da kujerar ‘dan majalisar dokoki na mazabar Surulere a jihar Legas, wannan karo ya sake samun tikiti a jam’iyyar APC.
Tun 2015 ‘dan wasan kwaikwayon ya zama ‘dan majalisa, akwai yiwuwar ya zarce har 2027.
4. Ned Nwoko
Ned Nwoko bai cikin matasa, amma shahararren mutum ne a Najeriya. Attajirin zai yi wa PDP takarar Sanata a mazabar Arewacin jihar Delta a zabe mai zuwa.
Mai kudin ya na auren taurariyar ‘yar wasar fim dinnan, Regina Daniels, su na da ‘ya ‘ya biyu.
5. Odi Okojie
Na karshe a jerin da Punch ta fitar shi ne Odi Okojie wanda ya samu tikitin takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a jihar Edo, yana so ya wakilci yankin Esan a 2023.
Odi Okojie ya yi suna, haka zalika mai dakinsa tun Mercy Johnson wanda tsohuwar ‘yar fim ce.