Mahaifi ya jefar da danshi mai shekara daya a daji ana tsakar sheka ruwan sama, duba dalili


Wani mutum mai suna Mr. Godwin Etim Aweh ya jefar da dan shi mai shekara daya da haihuwa a daji da ke kusa da gidansa ana tsananin sheka ruwan sama bisa zargin cewa yaron shu'umi ne da ke tare da Aljannu. Kafar watsa labarai na isyaku.com ya samo.

Lamarin ya faru ne a garin Odoro Nkit da ke karamar hukumar Esit Eket na jihar Akwa-Ibom.

Mr. Aweh yana sana'ar sarrafa barasa ne kuma kwatsam ya gaya wa matarsa cewa ya gaji da ganin yaron domin yana tare da Aljannu. Sakamakon haka ya jefar da yaron kuma ya dinga hanawa tare da yi wa matarsa duka duk lokacin da ta yi kokarin sake dauko yaron.

Wata kungiya mai zaman kanta ne ta ceto yaron kuma aka kai shi asibiti inda yake jinyar cutar mura da ciwon karaya a hakarkarinsa. Za a kuma yi masa tiiyata sakamakon kariyar.

"Mr. Aweh who runs a local wine business in Unyenge, Mbo local government area came home during the weekend and told his wife that he was no longer interested in having the child as his son anymore as the child is believed to be possessed by demonic powers

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN