Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Yan sandan jihar Sokoto sun damke matasa 3 bisa zargin mallakar miyagun ƙwayoyi da muggan makai


Rundunar yansandan jihar Sokoto ta ce ta kama wasu mutum uku bisa zargin mallakar miyagun ƙwayoyi da makamai a jihar. Shafin isyaku.com ya samo.

Wata takarda da Kakakin hukumar ya fitar wa Manema labarai ranar Alhamis 30 ga watan Yuni wanda shafin labarai na isyaku.com ya gani, (PPRO),  DSP Sanusi Abubakar, ya ce an cafke mutanen uku ne sakamakon bayanai da ayyukan sirri wajen gudanar da aikin Dan sanda. 

Ya ce an gudanar da irin wannan aikin ne domin a dakile yiwuwar yin amfani da matasa wajen horar da su domin aikata manyan laifuka musamman gabanin zabukan 2023.

ya ce wadanda aka kama sun hada da Mansur Yusuf, Bashiru Aliyu da Abdulwahid Zakari,

Ya ce an kama su ne lokacin da suke atisayen koyon yadda za su kaddamar da hargitsi da tashin hankali a cikin alummr jihar. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies