Asiri ya tonu: An kama jami'an tsaro suna waya da yan ta'adda bayan harin Kuje


Yanzu haka ana tsare da jami'an hukumar yan sanda biyu kan mummunan harin da yan ta'adda suka kai gida gyaran Halin Kuje a Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'adda, waɗan da suka ci ƙarfin jami'an tsaron gidan Yarin, sun kwance Fursunoni 800, ciki har da baki ɗaya mayaƙan Boko Haram da ke tsare.

Harin wanda aka kai rana ɗaya da wani farmaki da yan bindiga suka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Katsina, ya kaɗa hanjin yan Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa an yi ram da yan sandan guda biyu ne bayan sun tattauna da wasu daga cikin yan ta'addan da suka tsere ta wayar Salula.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa:

"Biyu daga cikin 'yan ta'addan da suka tsere daga gidan Yarin sun kira jami'in ɗan sanda mai bincike, (IPO) a ɗaya daga cikin Caji Ofis ɗin mu, kuma ya masa magana mai rikitarwa."

"A yanzun dai ana cigaba da bincikar su domin gano matakin haɗin kan da ka iya yuwu wa sun bayar."

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE