Rundunar Yan sandan Najeriya ta kori wani Safeton Yan sanda mai suna Richard Gele daga aiki bayan ya bayyana a wani faifen bidiyo yana karbar cin hanci yayin gudanar da sintirin binceken tsaro ranar 25 ga watan Yuli. Kafar labarai ya yanar gizo isyaku.com ya samo.
Kafin korarsa daga aikin Yan sanda an dauki Safeto Richard mai lambar aikin Dan sanda AP/No. 188547 a shekarar 2000. Kuma Yana aiki ne da sashen Yan sandan kwantar da tarzoma ta 77 da ke Birnin Okene aka tura shi aikin kula da lafiya da tsaron jama'a a hanyar Itobe zuwa Anyigba inda ya gamu da kaddarar da ta kawo karshen aikinsa ba girma ba arziki.
Kafin a kore shi daga aiki, an gurfanar da Richard a Kotun cikin gida na Yan sanda watau "Orderly room" inda aka kama shi da laifin saba tare da karya dokokin aikin Dan sanda sakamakon haka aka zartar masa da hukuncin kora daga aiki.
Latsa kasa ka kalli bidiyo da ya ja wa Safeto Richard Gele matsala...